Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fadakar Da Makiyaya Akan Mahimmancin Zaman Lafiya


Migrants react on the Serbian side of the border as Hungarian riot police fires tear gas and water cannon near Roszke, Sept.16, 2015. Police fired tear gas and water cannon at protesting migrants demanding they be allowed to enter from Serbia on Wednesday on the second day of a border crackdown.

Rikici tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya ya zama tamkar ruwandare gama gari kuma yana daya daga cikin lamuran da suka jefa arewa cikin rashin zaman lafiya

Matsalar makiyaya da manoma a jihohin arewacin Najeriya da kan kaiga asarar rayuka na cikin dalilan rashin samun zaman lafiya a arewa. An yi irin wadannan rigingimun a jihohin Filato, Binuwai, Kaduna, Nasarawa, Taraba da dai sauransu kuma babu inda ba'a yi kashe-kashe ba da asarar dukiyoyi da raba mutane da muhallansu. A wasu wurare ma hatta noma an kasa yi balantana kasuwanci.

Sabili da kawo karshen tashin tashinar ya sa hadakar kungiyar makiyayan Najeriya ta Miyetti Allah ta soma gangamin fadakar da Fulani makiyaya a rugagensu mahimmancin zama tare da kuma rungumar kiwon zamani. Shugabannin makiyayan suna kewaye jihohin Najeriya domin su sadu da Fulani su wayar masu da kawuna.

Kawo yanzu sun ziyarci jihohin Nasarawa, Binuwai da Taraba da jihar Adamawa. A taron da suka gudanar a jihar Adamawa sabon shugaban makiyayan Najeriya Ardon Zuru Alhaji Muhammed Kiruwa yace tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a wannan rangadin fadakarwar da suke yi. Tuni kuma suka fara yin ragistan duk makiyayan Najeriya domin sanin na asali da wadanda ke shiga rigar makiyaya su yi barna.

Ardo Kiruwa yace suna tafiya kauye kauye suna tara Fulani suna yi masu bayani. Yanzu an fara fahimtar cewa tashin hankalin da a keyi ba alheri ba ne. Su ma hukumomi an sanarda su cewa rashin ba Fulani matsayi ba alheri ba ne. Rashin sake masu hanyoyin shanunsu ba alheri ba ne. Yakamata a duba duk abubuwan dake haddasa tashin hankali.

Alhaji Yusuf Boso wani jigo a kungiyar makiyayan daga jihar Neja kuma mataimakin shugaban kungiyar na daya ya bada tabbacin cewa da wannan fadakarwar da suke yi batun fada tsakanin makiyaya da Fulani ya kare.

Yayin da yake yiwa makiyayan jawabi gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako yace lokaci yayi da makiyaya zasu rungumi kiwon zamani wanda yace shi ne zai rage rikicin dake faruwa tsakanin makiyaya da manoma. Ya umurci makiyaya da su zauna wuri daya su yi kiwon shanunsu kana gwamnati ta raba masu wuraren da basu zama gonaki ba.

Sabili da matsalar rigingimun da aka samu tsakanin Fulani da makiyaya a wurare daban daban ana harsashen za'a samu karancin abinci a wannan shekarar domin wasu da dama basu iya yin noma ba musamman a jihohin Bunuwai, Nasarawa da Taraba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG