Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fargabar Yunkurin Juyin Mulki A Burkina Faso


Shugaban Burkina Faso Paul-Henri Damiba a Djibo
Shugaban Burkina Faso Paul-Henri Damiba a Djibo

An ji karar harbe-harbe daga babban sansanin soja da kuma wasu unguwanni a babban birnin kasar Burkina Faso ranar Juma'a, kana an ji karar wata fashewa a kusa da fadar shugaban kasar, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.

Sojoji sun mamaye muhimman wurare da kuma hanyar zuwa fadar shugaban kasa, suka kuma toshe hanyoyin shiga ofisoshin gwamnati da gidan talabijin din kasar wanda ya dakatar da aiki, a cewar Reuters.

Nan take dai ba a san ko yunkurin juyin mulki ne ba ko a'a, amma lamarin na kama da juyin mulki da aka gani a wasu kasashen Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sojoji sun toshe hanyoyi a babban birnin Burkina Faso
Sojoji sun toshe hanyoyi a babban birnin Burkina Faso

Sojoji a karkashin jagorancin Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba sun karbi mulkin Burkina Faso a wani juyin mulki da aka yi ranar 24 ga watan Janairu.

Galibi farar hula ne suka yi farin ciki da juyin mulkin bayan da suka gaji da gwamnatin farar hula ta tsohon shugaban kasa Roch Kabore da ta gaza magance rikicin ‘yan ta’adda da suka kashe dubban farar hula a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, tare da kwace yankuna da dama na arewaci da gabashin kasar.

A jawabinsa na farko bayan juyin mulkin na watan Janairun da ya gabata, Damiba, wanda galibi ake gani a bainar jama’a sanye da kaki da tabarau, ya yi alkawwarin maido da tsaro.

Sai dai hare-hare a kasar da ke fama da talauci a Yammacin Afirka sun kara muni kuma sojojin na cikin rudani. Jami’an sojan da suka bai wa Damiba goyon baya a watan Janairu, sun nuna takaici kan rashin samun ci gaba, a cewar majiyoyin tsaro.

A wannan makon wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kashe sojoji 11 a wani hari da suka kai kan ayarin motoci 150 dauke da kayayyaki zuwa wani gari a arewacin Burkina Faso. Har yanzu ba a san inda farar hula 50 suke ba.

‘Yan bindiga sun toshe yankunan arewacin kasar, lamarin da ya sa al’ummomin yankunan shiga tsaka mai wuya. Ayarin motocin gwamnati da jiragen sama ne ke kai kayayyaki ga farar hular da suka makale.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG