Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana haramar fara bikin wasanin Olympics


Yan wasan Amirka ciki unifam dinsu na wasanin Olpympics

A yayida ake haramar fara wasani Olympics wani dan kasar Sudan ya nemi mafakar siyasa

An bada rahoton cewa wani dan kasar Sudan dake yin gasar gudu wajen wasani Olpmpics ya bukaci Ingila ta bashi mafakar siyasa.

An bada rahoton cewa a farkon wannan makon, shi wanna dan kasar Sudan din ya shiga wani ofishin yan sanda yana bukatar a bashi mafakar siyasa. To amma kamfanin dilancin labarun Associated Press ya ambaci wata sanarwar ofishin jakadancin Sudan dake musunta wannan al’amari.

Tunda farko a yau juma’a sanannen agogon London nan Big Ben yayi ta bugawa har sau arba’in cikin mintoci uku, sa’anan coci suka buga kararwarsu motocin kuma suka yi nasu ham din domin yiwa fara wasanin Olympic shekarar dubu biyu da goma sha biyu, maraba.

Makakken agogon dake kan wata husumiya dake kalon ginin Majalisar dokokin Ingila, ya fara bugawa ne da misalin karfe takwas da mintoci goma sha biyu na safe agogon Ingila.

An yi jigilar tocin Olmpics cikin jirgi ruwan Gloriana na sarakan kasar akan kogin Thames zuwa gandun Olmpics a birnin London.

Yau juma’a da maraice agogon London tocin zai gama tafiyarsa a yayinda za’a kuna shi a wajen bikin bude wasanin Olympics din.

Kimamin yan wasa dubu goma ne zasu yi gasa yayinda da dubban mutane zasu ziyarci London domin kalon wasanin Olpmpics din. A hukunce sarauniyar Ingila Elizabeth zata bude wasanin. Za’a yi gasar har zuwa ranar goma sha biyu ga watan Augusta.

Kimamin jami’an tsaro dubu talatin da shidda da suka kunshi sojoji da yan sanda da kuma wadanda aka yi hayansu ne ke gadin wuraren wasani Olmpics da tituna a birnin London da titunan wasu biranen Ingila.

XS
SM
MD
LG