Accessibility links

Ana Iya Kawar Da Polio Kamar Yadda Aka Kawar Da Agana Da Kurkunu

  • Garba Suleiman

Yaki da Cutar Shan Inna a Najeriya

Masana a zauren taron da Muryar Amurka ta shirya sun yi nuni da nasarorin da aka samu wajen kawar da wasu cututtukan

Masana a zauren taron da Muryar Amurka ta shirya kan yaki da cutar Polio, sun ce nasarorin da aka samu a can baya wajen kawar da cututtuka kamar agana da kurkunu a nan kusa, alamu ne dake nuna cewa ita ma cutar shan inna ta Polio za a iya kawar da ita.

Masanan suka ce a wancan lokacin ma, mutane sun yi ta nuna turjiya a lokacin da ake kokarin kawar da cutar agana baki dayanta, amma daga baya da suka gane amfanin rigakafin, jama'a sun rungume shi hannu bibbiyu, aka kuma samu nasara.

A cikin 'yan kwanakin nan, jami'an lafiya na duniya sun zaga Najeriya baki daya kaf, amma ba a samu rahoton mai fama da cutar kurkunu ba ko guda daya, abinda ya sa a yanzu aka ayyana Najeriya a zaman wadda ta kawar da cutar. Wannan ma an samu nasarar hakan ne ta hanyar rigakafi.
XS
SM
MD
LG