Accessibility links

Ana Jiran Hukuncin Kotu Kan Shari'ar Fara Minista Nawaz Sharif


An kawo karshen sauraron shari'ar da ake yiwa Fara Ministan Pakistan kan aikata laifin cin ranci da rashawa.

Kotun kolin Pakistan ta kawo karshen sauraron karar aikata cin hanci da rashawa da ka iya sauke Fara Minista Nawaz Sharif ta kuma haramta masa tsayawa takarar siyasa a kasar.

Alkalai ukun da suka saurari karar basu fadi lokacin da zasu sanar da hukuncin da suka yanke ba.

Da yake jawabin karshe, ‘daya daga cikin alkalan yayi alkawarin cewa zasu duba yiwuwar haramtawa Sharif shiga duk wasu harkokin siyasa a wani bangare na shari’ar.

Sharif dai ya musanta aikata duk wani laifi, matsayin da lauyoyinsa suka yi ta nanatawa a lokacin wannan shari’ar da ta kwashe mako guda ana yinta.

Sai dai kumalauyan dake wakiltar jam’iyyar da ta shigar da ‘kara ta Tehreek-e-Insaf, na da kwarin gwiwar cewa za a samu Fara Ministan da aikata laifi a kuma haramta masa shiga duk wasu harakoki na siyasa.

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG