Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa a Girka Ta Yi Sanadiyar Rayuka Da Lalata Gine-gine


Girgizar kasa a Girka

Da safiyar yau Juma’a wata girgizar ‘kasa mai karfin maki 6.7 ta kashe a kalla mutane biyu ta kuma raunata sama da mutane 100 a tsibirin Kos na kasar Girka.

Jami’an Girka sunce mutanen biyu da suka mutu masu yawon bude ido ne daga kasashen Sweden da Turkiyya, amma basu bayyana sunayensu ba.

A kalla mutane biyar sun samu munanan raunuka, an kuma ‘daukesu ta jirgi mai saukar ungulu zuwa Asibitin tsibirin Crete.

Jami’an agajin gaggawa na Turkiyya sun gargadi mutane game da girgizar ‘kasar da ka iya biyo bayan wadda ta faru, amma sunce ba a samu asarar rayuka ko mummunar barna ba a Turkiyya.

Masu aikin ceto kuma sunci gaba da neman mutanen da suka makale a gidajensu bayan da girgizar kasar ta afkawa yankin da missalin karfe 1 da rabi na dare.

Magajin garin Kos Giorgos Kyritsis, ya ce yawancin gidajen da abin ya shafa tsaffin gidaje ne, da basu cika ka’idojin da doka ta samar na tabattarda ingancin gine-gine ba ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG