Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jiran Sakamakon Zaben Ghana


Zaben Ghana

Yanzu haka dai ana zaman ‘dar ‘dar a kasar Ghana biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar jiya Laraba, wanda yanzu haka ake jiran sakamakon zaben daga hukumar zabe ta kasar.

Magoya bayan bangarorin manyan jam’iyyun kasar biyu wanda suka hada da magoya bayan John Mahama dake kan karagar mulki a yanzu kuma ke neman zama shugaban kasa a karo na biyu da kuma magoya bayan shugaban yan adawa Nana Akufo-Addo wanda ya sha kaye a zaben da akayi shekaru hudu da suka gabata.

Baki daya magoya bangarorin biyu kowa na ikirarin sune suka lashe zaben duk kuwa da cewa har yanzu hukumar zabe mai zaman kanta bata fitar da sakamakon zaben ba tukunna.

Rahotanni na cewa akwai wasu wurare da ba a samu kada kuri’a jiya Laraba sakamakon rashin isar kayayyakin aiki, wanda kuma sai yau Alhamis za’a bude musu runfunan zaben domin mutanen yankunan su kada kuri’unsu.

A wata hira da Muryar Amurka tayi da jakadan wanzar da zaman lafiya a Ghana, Irbad Ibrahim, wanda yace yanzu haka mutane basu fito harkokinsu na yau da kullum ba domin tsoron abin da ka iya faruwa, biyo bayan ikirarin samun nasarar zaben da bangarorin manyan jam’iyyun biyu ke yi.

Domin karin bayani ga hira da Jakadan wanzar da zaman lafiya Irbad Ibrahim.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:13 0:00

XS
SM
MD
LG