Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ka-Ce-Na-Ce Kan Kudaden Da EFCC Ta Kwato a Hannun Kamfanonin Mai


Tambarin Hukumar EFCC a Najeriya

Lauyoyi da kungiyoyin rajin yaki da rashawa da tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya na ci gaba da tsokaci dangane da kudaden basussuka da hukumar EFCC ta ce ta kwato fiye da naira biliyan 328 daga hannun manyan kamfanonin dillancin mai.

Bayan da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta bayyana cewa ta gano wasu makudan kudade na basussuka a hannun manyan kamfanonin mai a kasar, masana da kungiyoyi tabbatar da adalci n ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

Yayin da wasu ke yaba wannan mataki wasu kuwa cewa su ke hukumar ta EFCC ta yi shisshigi domin ba huruminta ba ne wajen karbo basukan da gwamnatin Najeriya ke bi.

A farkon makon nan ne shugaban hukumar ta EFCC a shiyyar arewa maso yammcin Najeriya da ke Kano, Dr. Adamu Hamisu Dan Musa ya bayyanawa manema labarai cewa sun kwato akalla biliyan 328 daga hannun kamfanonin.

“Wannan abu ne mai kyau a ce ana samun dawo da kudade makudai irin wadannan da aka yi almundahana da su aka ci amanar kasa.” In ji Comrade Nura Iro Ma’aji, jami’i a kungiyar CISLACmai tabbatar da adalci.

Sai dai Iro Ma’aji ya kara da cewa, lokaci ya yi da gwamnati za ta yi “karatun ta nutsu” domin a cewarsa, abu ne da ake yi da sanin wasu jami’an gwamnatin.

Amma wasu masana a fannin dokoki suna ganin ba hurumin hukumar ta EFCC ba ne ta je ta na karbo kudaden bashi da gwamnati ke bi.

“Idan maganar doka za a yi EFCC ta aikata haramun, idan ka duba dokar da ta kafa ta a shekarar 2007, kwata-kwata ba ta da hurumin ta shiga maganar bashi.” A cewar Barrister Audu Bulama, lauya a jihar Kano.

Saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Mauryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG