Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kururuwar Rashin Tsaro Da Tsadar Rayuwa a Arewacin Najeriya


Shugaban Yan Saandan Nigeria, Muhammaed Adamu Abubakar
Shugaban Yan Saandan Nigeria, Muhammaed Adamu Abubakar

Yayin da miyagu ke ta cin karensu ba babbaka a arewacin Najeriya mai fama da tsadar rayuwa, jama'ar yankin - kama daga masu fada a ji zuwa talakawa - na ta wayyo Allah.

Batun kalubalen tsaro da tsadar rayuwa da kuma tabarbarewar tattalin arziki, na ci gaba da yin mummunan tasiri kan ‘yan Najeriya, musamman mazauna yankin arewacin kasar. Yanzu haka dai dattawa a yankin arewa da sauran masu ruwa da tsaki na bayyana matakan bi domin lalubo mafita.

Al’amarin baya bayan nan, shi ne yadda batagari ke satar mutane domin karbar kudin fansa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, baya ga farmarkin da tsageru ke kaiwa Kauyuka da garuruwa a jihohin Kastina, Zamfara da Sokoto da dai sauransu.

BAUCHI: 'Yansandan Bauchi sun kama masu satar mutane
BAUCHI: 'Yansandan Bauchi sun kama masu satar mutane

Yanzu haka dai masu sharhi na ci gaba da jan hankalin mahukunta kan bukatar karkata hankulansu game da halin da lardin na arewa ke ci. Honorabul Nasiru Garba Dantiye tsohon wakili a zauren Majalisar Dokokin Najeriya, na daya daga cikin wadanda ke bayyana damuwarsu kan wannan al'amarin.

To amma Dattijo Abdulkarim Dayyabu da ke zaman 'kwamandan' Rundunar Tabbatar Da Adalci a kasar, na cewa, Shugaban Ma’aikata a Fadar Gwamnatin Tarayya shi ke da muhimmiyar rawar takawa wajen daidaita tafiyar gwamnatin Najeriya.

Wasu Masu Fashi Da Garkuwa Da Mutane Domin Kudin Fansa Da 'Yan Sanda Suka Kame.
Wasu Masu Fashi Da Garkuwa Da Mutane Domin Kudin Fansa Da 'Yan Sanda Suka Kame.

Sai dai shugabannin siyasa irin su tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido na ganin lokaci ya yi da ya kamata jagorori, musamman ma a lardin na arewa, su fada wa juna gaskiya da nufin daidaita lamura.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00


XS
SM
MD
LG