Ana kyautata zaton an kashe Da kuma magajin wanda ya kafa kungiyar al-Qaida Osama bin Laden, ana tunanin wani hari da Amurka ta taimaka aka kai ne ya yi sanadiyar mutuwarsa, a cewar wasu rahotanni.
Jami’ai da suka yi bayani akan batun amma suka so a sakaya sunansu, sun tabbatar da mutuwar Hamza bin Laden, wanda ake zaton shekarunsa 30 da haihuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran NBC ya fada a jiya Laraba.
Daga baya jaridar New York Times ta ba da rahoton cewa tun cikin shekaru biyu da suka gabata aka kashe Hamza bin Laden a wani farmaki wanda kusan da taimakon Amurka aka kai shi.
Amma jami’ai sun fadawa jaridar ta Times cewa gwamnati ba ta tabbatar da mutuwar Hamza ba kuma ta ki ta yi karin bayani.
Dama Amurka ta sha sanar da ba da tukwicin har dala miliyan 1 ga duk wani mai bayanin da zai kai ga kama Hamza bin Laden ko kashe shi, wanda ke tare da mahaifinsa a lokacin da kungiyar al-Qaida ta kawo hari a nan Amurka a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001.
Kungiyar ta A Qaida, ta kai hare-haren ta’addanci akan katafaren benen cibiyar cinikayya ta duniya da ke birnin New York da kuma ginin ma’aikatar tsaron Amurka na Pentagon.
Bisa ga wasu wasiku da aka samo a gidan Osama bin Laden a garin Abbottabad da ke Pakistan, an horar da Hamza bin Laden tun yana yaro don wata rana ya jagoranci kungiyar ta’addancin mahaifinsa.
Facebook Forum