Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Duk ‘Yan Gudun Hijirar Najeriya Za Su Koma Garuruwansu


ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu
ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu

Kwamitin raya yankin arewa maso gabas na bukatar Naira Tiriliyan biyu cikin shekaru goma, don aikin raya yankin arewa maso gabas da hakan zai baiwa dukkan wadanda suka rasa muhallansu damar komawa garuruwansu na asali.

Ya zuwa yanzu dai an ware kusan Naira miliyan 500 don tallafawa jama’a su kama sana’ar Noma da samar da kiwon lafiya da matsugunnai ga jama’a, a cewar mataimakin shugaban kwamitin raya yankin arewa maso gabas Alhaji Tijjani Tumsa.

A kwarin gwiwar a Tijjani Tumsa ya nuna, kwamitin da Janar T. Y. Dajuma ke jagoranta na sa ran nan bada dadewa ba dukkan jama’ar da suka rasa matsugunnai da kuma ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira zasu koma gida.

Yanzu haka dai kwamitin na aiki ne da kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar wanda akalla yanzu ya kai sama da Naira Biliyan 10.

Haka nan kwamitin ya ce wani harin da ‘yan Boko Haram suka kai a masallaci a garin Bama da ya yi sanadiyar rayukan mutane bakwai, bai karya gwiwar jama’a masu aniyar komawa garuruwansu na asali ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG