Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC ta Cafke Muntari Shagari Da Wadansu Kan Kudaden Da Diezani Allison-Madueke Ta Kwasa


Tsohuwar Minista Dizeani Madueke
Tsohuwar Minista Dizeani Madueke

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta gurfanar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Sakkwato Muntari Shagari a babbar kotun tarayya da ke Sakkwato tare da shugaban jamiyyar PDP na Jihar Ibrahim Milgoma da tsohon dan takarar gwamna Abdalla Wali da wasu jiga-jigan jam'iyyar Ibrahim Gidado da Nasiru Dalhatu Bafarawa.

Ana tuhumarsu da laifuka 5 da suka kunshi badakalar kudi ta tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madueke aka ce adadinsu ya kai Naira miliyan 500.

Jagoran lauyoyin hukumar EFCC a zaman kotun, Barrister Johnson Ojogban ya ce ana zarginsu ne da sama da fadi da kuma rarraba kudi Naira miliyan 500 jim kadan kafin zaben shekarar ta 2015 ba tare da amfani da hukumomin hada-hadar kudade da suka kamata ba.

An kuma rarrabasu ba ta hanyar banki ba, kuma kudaden da ake zargin Diezani tayi awon gaba da su ta kuma rarrabasu kafin gudanar da zaben shekarar 2015.

Duk wadanda ake zargi sunki amsa laifin da ake tuhumarsu da shi, an kuma dage sauraron karar zuwa jibi Alhamis domin yanke hukuncin kotu dangane da bukatar bada belin wadanda ake tuhuma.

Alkali kuma ya bada umarnin ci gaba da tsaresu a ofishin 'yan sandan jihar ta Sakkwato har zuwa ranar Alhamis.

Lauyan wanda ake zargi, wato tsohon mataimakin gwamnan jihar ya ce bada beli ra'ayi ne na kotu, amma yanzu suna da sa'oi 48 domin yanke hukunci. Sannan kuma abin da ya faru yayi dai dai da lamarin doka.

Hukumar EFCC Ta Danke Muntari Shagari
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG