Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Samun Karin Hadin Kai Tsakanin Amurka Da Masar A Yaki Da Taaddanci


BELGIUM -- U.S. Secretary for Defense Jim Mattis (L) speaks with NATO Secretary-General Jens Stoltenberg prior to a meeting on the sidelines of a NATO defense ministers meeting at NATO headquarters in Brussels, November 8, 2017

Sakataren harkokin tsaron Amurka ya jaddada hadin kan dake tsakanin Amurka da Masar game da yaki da taadanci yana kara bunkasa.

Sakataren tsaron Amurka Chief Jim Mattis ya fada cewa hadin kan dake tsakanin Amurka a Masar game da taaddanci sai kara habbaka yake yi.

Yace Amurka har kullun a shirye take ta samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin ta da Cairo duk ko dakile wasu taimakon sojan da akayi zuwa Masar din a farkon wannan shekarar.

Mattis dai yana Magana ne a babban birnin kasar ta Masar sailin da ya yada zango akan hanyar sa zuwa kasashe 4 da zai tafi ran gadi, wato kasashen dai sun hada da ita kanta Masar, Jordan,Kuwait, da Pakistan.

Wannan ziyarar dai tazo ne dai-dai lokacin da sojojin Amurkan suka mayar da hankalin su ga kasashen gabas ta tsakiya bayan sunyi nasarar fatattakar kungiyar ISIS, daga inda suke ikirarin nan ne tungar su da suka kafa daular islama wato Iraqi da Syria.

Daya daga cikin abinda wannan ziyarar tasa zata fi mayar da hankali ko shine matsa wa kasar Pakistan lamba data kawo karshen huldan ta da ‘yan taadda da ake zargin tanayi wanda har suke kaiwa sojojin hadin gwiwar Amurka da Afghanistan hari.

Mattis ya shaidawa manema labarai cewa munji cewa kasar ta Pakistan na cewa ita bata mara wa ayyukan taadanci baya to fata shine mu gani a kasa, ta hanyar aiwatar da manufofin ta.

Ko a cikin watan Oktoban nan data shige sai da mattis yace Amurka zata sake baiwa kasarta Pakistan din wani kari daman a wurin yin aiki da ita kafin ta yanke hukunci akan ko da gaske ne tana da alaka a ‘yan taadda ko kuma a’a.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG