Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saura Kwana Hudu Kafin Zabe: Me 'Yan Takarar Shugabancin Amurka Suke Cewa Ne?


Shugaban Amurka Brack Obama da uwargidansa Michelle, da kuma abokin takararsa Mitt da Ann Romney.
Shugaban Amurka Barack Obama ya koma fagen yakin neman a sake zabensa, bayan mako daya yana jagoran shirye shiryen gwamnatin tarayya dangane da bala’in guguwar “Sandy.”
Shugaban dan jam’iyyar Democrat, ya yi yakin neman zabe a jihohin Wisconsin, da Nevada, da Colorado jiya Alhamis. Jihohi uku da suka cikin rukunin jihohi da ake yiwa lakabin “mazari”, wadan nan jihohi duk wanda ya sami nasara a cikinsu, zai lashe zaben shugaban kasa da za a yi ranar Talata.
Shugaba Obama da abokin takararsa Mitt Romney a wani zaman muhawara da suka yi.
Shugaba Obama da abokin takararsa Mitt Romney a wani zaman muhawara da suka yi.

Mr. Romney yayi yakin neman zabe a jihar Virginia, daya daga cikin jihohin da suke da muhimmancin gaske a zaben da za a yi ranar 6 ga wata.

‘Yan takaran duka biyu sun caccaki shiryen shiryen juna na inganta tattalin arzikin Amurka wanda ahalin yanzu bashi da kwari.Mr. Romney ya gayawa magoya bayansa a Roanoke cewa, ‘yan tsaka-tsaki suna fuskantar matsin rayuwa na kudi a mulkin shugaba Obama. Yace samu ya ragu, yayinda bukatun yau da kullum kamar mai da kiwon lafiya farashinsu sun karu.

Da yake magana ga magoya bayansa a Las Vegas, a jihar Nevada shi kuma, shugaba Obama ya gayawa magoya bayansa cewa, shirye- shiryen tattalin arziki da Mr. Romney yake tallatawa, masu hanu da shuni ne zasu fi amfana karkashin shirin, manufofi da yace sun gaza a baya. Shugaban ya kwabi abokin hamayyarsa sabo da gabatar da wadan nan manufofi a matsayin “canji”.

Jiya Alhamis, magajin garin New York Michael Bloomberg, ya bayyana goyon bayansa ga shugaba Obama a yunkurin shugaban na neman wa’adi na biyu. Magajin garin ya ambaci kokarin Mr. Obama na yaki da gurbatar yanayi, daga motoci da masana’antu. Masana kimiyya sun ce hayaki daga motoci suna taimakawa wajen jawo dumamar yanayi, watakil harda irin mahaukaciyar guguwarda da tayi barna a baya-bayan nan, watau Sandy.

Shugaba Obama yace goyon bayanda magajin garin ya bashi babbar karramawa ce. Mr. Obama yace kodasahike ra’ayinsu bai zo daya ba kan ko wani lamari, duk da haka dukkansu biyu suna goyon bayan inganta ilmi, garambawul ga shirin shige da fice, da kuma yaki da sakewar yanayi.
XS
SM
MD
LG