Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Saye Filayen Makiyaya Da Manoman Nijar


‘Ya'yan Fulani

Matsala tsakanin makiyaya da manoma ba sabon al’amari bane a kasashen Afirka ciki kuwa har da kasar Nijar, amma wannan karon suna neman kwatar kansu ne game da filayen noma da kiwon dabbobi.

Masu hali sun dauki sabon salon saye manyan gonakai da filayen kiwon dabbobi, inda hakan ya fara tada hankalin mutanen karkara makiyaya da manoma kamar yadda wasunsu suka bayyana.

Wani mai Magana da yawum fulanin ma cewa yayi, suna nan suna jan hankalin mutanensu daga yarda da masifar sayar da filayen da a da ake amfani da su wajen kiwon shanunsu.

Jama’ar karkarar sun bullo da yin wani taro ne don tabbatar da dau mataki a shari’ance saboda yiwa tufkar hanci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG