Accessibility links

Ana shirin fara yakin neman zaben watan Afirilu a Mali

  • Ibrahim Garba

Wasu ma'aikata a birnin Bamako na nuna kiyayya ga kiraye-kirayen mulkin soja

Ana nan ana shirin fara yakin neman zabe a kasar Mali don

Ana nan ana shirin fara yakin neman zabe a kasar Mali don zaben sabon Shubaban kasa adaidai lokacin da ake fama da boren Asbinawa.

Kimanin ‘yan takara 20 ne ke sha’awar gadar shugaba mai ci Amadou Toumani Toure, wanda ba zai tsaya takara ba bayan ya yi wa’adi biyu.

An tsayar da ran 29 ga watan Afrilu don yin zaben. Wani madugun ‘yan adawa da ke takara , wato tsohon Firayim Minista Ibrahim Boubacar, ya yi watsi da fargabar da ake nunawa cewa tashin hankalin na arewacin Mali zai kawo tangarda ga zaben.

“Akwai sarari sosai, don haka za mu yi zabe a karshen watan Afirilu kuma ana kwanan nan za a fara shirye-shirye. Yau mun nuna wa duniya cewa mu kasa ce mai goyon bayan dakarunta da su ka je arewacin Mali don su kare martabarmu a matsayin al’umma, saboda babu wata tantama game da taswirar kasar Mali.” A cewarsa.

‘Yan awaren Asbinawa sun fara kai hare hare kan sansanonin soji da ke cikin hadamar Mali tun cikin watan Janairu. Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijira ta MDD ta ce tashin hankalin ya raba mutane 130,000 a ciki da kewayen Mali da muhallansu.

Wani dan takaran kuma da ake ganin zai taka rawar gani a zaben, wato tsohon shugaban kungiyar dalibai Oumar Mariko, y ace yakamata ‘yan takaran su maida hankali kan batutuwan habbaka kasar, ciki har da bangarorin ilimi da kiwon lafiya.

XS
SM
MD
LG