Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Gudanar Da Sabuwar Tattaunawa Kan Rikicin Syria


Ministan harkokin wajen Rasha Sergie Lavrov ya na gaisawa da bangaren 'yan adawan Syria

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, Steffan de Mistura, ya ce yana fatan sake fara wata sabuwar tattaunawa kan samar da zaman lafiya  a Syriya a ranar 20 ga watan Fabrairu.

An ayyana zaman sasantawar a Geneva ne da fari a ranar 8, ga watan Fabrairu, amma Mistura ya bayyana cewa baya tunanin abokan adawa za su iya ba da jerin sunayen wakilansu kafin ranar 8 ga watan na Fabrairun.

Ya kuma ce idan har bai samu jerin sunayen nan da ranar 8 din ba, zai ba da sunayen sannan da kansa kuma zai tabbata an samu wakilcin kowa da kowa.

De Mistura ya bayyanawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ci gaban da aka samu akan samar da zaman lafiyar, wanda ya hada da tattaunawar da aka yi tsakanin Sojojin 'Yan tawaye da Gwamnatin Syria a Kazakhstan.

Wannan zaman ya kammala da amincewar Rasha da Turkiya da Iran inda suka yadda su zama masu saka ido a takaitacciyar tsagaita wutar da aka yi a watan Disamba.

Kwamitin Tsaro na Majalisar ya ce tattaunawar da aka yi a Kazakhstan wani ci gaba ne domin karfafa tsagaita wutar da aka cimma inda ake fatan za ta share hanyar da za’a samar da mafita a siyasance akan rikicin da aka kwashe shekaru shida ana gwabza shi.

XS
SM
MD
LG