Hakan ya biyo bayan kammala gabatar da hujjojinsu da lauyoyin Trump suka yi a ranar Juma’a, inda suka musanta cewa shi ya tunzura maharan da suka far wa ginin majalisar dokokin kasar.
Lauyoyin har ila yau sun ce shari’ar bi-ta-da-kullin siyasa ne.
Lauyoyin tsohon shugaban sun kwashe sa’a uku a ranar Juma’a suna kare shi, maimakon sa’a 16 da aka ba su.
Har Ila yau, sun fadawa sanatoci cewa tsohon shugaban na da ‘yancin ya kalaubalanci kayen da ya sha a hannun shugaba Joe Biden, suna masu cewa, jawabin da ya yi na minti 70 gabanin mamayar da aka yi wa majalisar dokokin a ranar 6 ga watan Janairu, bai ci a ce ya tunzura jama’a ba.
Tun a farko-farkon sauraren wannan shari’a a, ‘yan Demmocrat suka gabatar da hujjojin da suke nuni da cewa Trump ne ya tunzura masu boren.
Dubi ra’ayoyi
Ko ka yi rijista da mu? Shiga shafinka
Ba ka yi rijista da mu ba? Yi rijista
Load more comments