Ana sa ran a ranar Asabar, sanatoci a majalisar dattawan Amurka za su saurari muhawarar karshe kan shari’ar tsige tsohon shugaba Donald Trump.
Mafi yawan ‘yan Republican a majalisar dattawan Amurka sun kada kuri’a jiya Talata game da kin amincewa da gudanar da shari’ar tsige tsohon shugaba Donald Trump.
Ana shirin rantsar da ‘yan Majalisar Dattawan Amurka a matsayin alkalai da kuma masu taimaka musu a shari’ar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.
An rantsar da Dan Jam’iyyar Democrat Joe Biden, a yau Laraba a matsayin shugaban Amurka na 46 a Majalisar Amurka.
Ku kalli Shan Rantsuwar Joseph R. Biden da Kamala D. Harris da Za’a yi a Washington. Ranar Laraba 20 ga Watan Janairu Daga Karfe 11:30 na Safe Agogon Washington DC
Hukumomi a Amurka sun tsaurara matakan tsaro a birnin Washington DC yayin da ya rage kwanaki a rantsar da zababben Shugaba Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46.
Zababbaen shugaban Amurka Joe Biden ya ce “a gwagwarmayar kare Amurka, Dimokradiyya ta yi nasara,” a jawabin da yayi ranar Litinin, jim kadan bayan da wakilai na musamman suka tabbatar da zaben sa a matsayin shugaban kasa.shugabancinsa.
Wannan na zuwa ne yayin da Joe Biden ya damka wa mata sashen sadarwar fadar White House
Zababben shugaban Amurka, Joe Biden da Mataimakiyar Shugaban mai jiran gado Kamala Harris, sun sanar da nadin tawagar mata zalla a fannin sadarwa.
Hukumar da ke hidima ga cibiyoyin gwamnatin tarayyar Amurka (GSA a takaice), ta tabbatar cewa zababben shugaban kasa Joe Biden, shi ne a ta bakinta, “wanda, ga alama ya yi nasara” a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.
Masu zanga zanga sun yi taro a Washington a jiya Asabar domin nuna goyon baya ga shugaba Donald Trump da zargin da ya yake yi na tabka magudi a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba da babu hujja.
Jiya Lahadi, a karon farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna ya amince da cewa dan takarar Demokrat Joe Biden "ya lashe" zaben shugaban kasa kusan makonni biyu da suka gabata, amma sanadiyyar magudi.
Domin Kari
No media source currently available
Ana amfani da jirage marasa matuka a kullum wajen yaki, tabbatar da bin doka da kuma aikin gona. Amma yanzu ana samun karuwar masu sana’o’i a Amurka dake amfani da jiragen marasa matuka wajen kai wa mutane biskit da shayin gahwa har kofar gidajensu.
A Kenya wani shirin na afuwa ga makiyaya da suka dawo da makamai dake hannunsu, bayan wasu munanan hare-hare da barayin shanu da 'yan fashi suka kai a arewacin jihar Rift Valley, bindigogi kalilan ne aka samu mayarwa ga hukuma yayin da makiyayan suka ce suna bukatar kare kansu.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar kungiyar ECOWAS, EU da Majalisar Dinkin Duniya, sun fara wani aikin karbe makamai da mutane ke rike da su ba bisa ka’ida ba a fadin kasar.
Bayan shiru na wasu kwanaki tun bayan hukuncin kotun kolin kasar, babban bankin Najeriya ya umurci bankuna a kasar da su ci gaba da mu’amala da tsofaffin takardun kudi na naira 200, da 500 da dubu daya har zuwa karshen wannan shekara.
Hukumomin lafiya a Ghana sun fara kai allurar rigakafin cutar kyanda a cibiyoyin kiwon lafiya domin shawo kan barkewar cutar da ya zuwa yanzu ta kama mutane 120.
Dr. Sa'adou Habou, likitan kwakwalwar a sashen dake kula da masu tabin hankali a babban asibitin Maradi, ya yi mana karin bayani a game da lalurar ta’ammali da miyagun kwayoyi.