Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ta Cece Kuce AKan Kin Saka Hannu Kan Kasafin Kudin 2021 Da Majalisan Najeriya Tayi.


Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila

A Najeriya, 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki na cece-kuce akan matakin da kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya dauka na kin sa hannu a kasafin kudin badi har sai an biya Kungiyar  Malaman  Jami'o'i kudadensu,a kuma biya wadanda ‘yan sanda suka kashe shekaru 10 da suka wuce diyya. 

Shugaban Majalisar Wakilai a Najeriya, Femi Gbajabiamila yayi wanan furucin ne a daidai lokacin da Majalisar ke fara aiki akan kasafin kudin shekara 2021 da Shugaba Mohammadu Buhari ya mika wa Majalisar.

Kakakin ya ce, lallai sai an biya diyar wadanda aka yi zargin ‘yan sanda sun kashe a kasar tun shekaru 10 da suka wuce kuma har ila yau sai an biya Kungiyar malaman jami'o'i da a halin yanzu suke yajin aiki dukannin kudaden da aka yi masu alkawalin za a biya tun a zamanin gwamnatin da ta shude.

Wani abu da Shugaban Jamiyar Accord, Mohammadu Lawal Nalado yace akwai abin dubawa a wannan furuci na Kakakin Majalisar domin idan ba a sa hannu a kasafin kudi ba, yana nufin ba za a yi wa 'yan kasa aiki ba ke nan, kuma yana kira ga gwamnati da ta dauki matakin tabbatar da amincewa da wanan kasafin kudi saboda a tsira daga matsalolin da akasin hakan ka iya jawowa.

A nashi nazarin, tsohon ma'akacin gidan rediyon BBC kuma a yanzu mai nazari akan al'amuran yau da kullum Bala Ibrahim, ya ce irin wanan furuci da ya fito daga bakin kakakin majalisar wakilai kuma daya daga cikin jigajigan Jamiyar APC mai mulki abin takaici ne.

A ganinsa idan har an biya masa bukata a ta hanyar biyan diyar da ya fada, to Bala ya ce yana da jadawalin mutanen sama da dubu daya na shiyar Arewa da tashin hankali ya same su kuma yake ganin su ma sai an biya masu diya.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a zauren Majalisar bayan an kamala aiki akan kasafin kudin na shekara 2021.

Saurari Cikakken Rahoton Medina Dauda cikin sauti:

#ENDSARS: Ta Bakin Masu Ruwa Da Tsaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG