Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Lauretta Onoche A Matsayin Kwamishiniyar Hukumar Zaben Najeriya Na Shan Suka


Shugaba Muhammadu Buhari

Nadin Lauretta Onoche wata hadimar Shugaban Najeriaya Muhammadu Buhari a matsayin Kwamishiniyar Zabe a kasar ya haddasa ka-ce -na-ce cikin al’umma.

A Najeriya har yanzu batun aika sunan hadimar Buhari, Laureta Onoche a matsayin kwamishiniya a hukumar Za6e ta kasar na cigaba da jawo cece kuce inda jamiyyun adawa irin su PDP da PRP da ma wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka tofa albarkacin bakunan su a wannan nadi da shugaba Buhari ya ke so ya yi.

A wata takarda mai dauke da sa hanun shugaban Kungiyar Marubutan Kare Hakin Dan Adam HURIWA, Emmanuel Onwubiko ya ce tuni ya maka Shugaba Buhari a Kotu akan neman ya janye wanan bukata ta shi na nada Laureta Onoche a wanan mukami.

Jamiyar adawa ta PRP dauke da sa hannun shugabanta, Alhaji Falalu Bello ta ce ba daidai ba ne shugaba Buhari ya yi irin wanan yunkuri domin hadimar ta shi yar jamiyar APC ce saboda haka wane irin aiki yake so ta je ta yi a hukumar za6e?

A wani bangaren kuma tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Bauchi Shuaibu Abubakar Ismail yayi nazari cewa wanan nadi dama ce ta shugaba Buhari kuma dole ne sai majalisar kasa ta tatance ta kafin mukamin ya tabbata.

Yana gani wanan mata ta cancanta ne shi yasa aka nada ta tareda fatan ba za ta ba shugaba Buhari kunya ba.

Tuni dai Kungiyar rajin kare mutuncin Najeriya, Concerned Citizens ta ce ta aika da takardar korafi akan nadin na Buhari zuwa Ingila da Amurka inda ta nemi a kawowa Najeriya dauki akan wai shugaba Buhari na neman lalata siyasar kasar ne.

Saurari rahoton Medina Dauda cikin sauti:.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00


Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG