Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ta Kokarin Ceto Yaran Da Suka Makale Cikin Kogo A Kasar Thailand


Hasashen da aka yi na cewa za’a sake samun ruwan sama “kamar da bakin kwarya” gobe Juma’a, ya kara jefa jami’an kasar Thailand cikin hanzarin kokarin ceto tawagar wasu matasa 12 ‘yan kwallon kafa da suka makale a cikin wani kogon wanda ruwa ya toshe hanyoyin shiga da fita nashi.

Wannan yasa ma’aikatan bada agaji dake famar tsamo yaran suka warwatsu a yau Alhamis don neman wasu hanyoyin na daban da zasu fito da su daga cikin kogon mai suna Tham Luang, wanda ake kokarin bude hanyoyinsa don ruwan dake ciki ya fice.

Yaran dai tun ran 23 ga watan jiya na Yuni suke cikin kogon bayanda ruwa ya toshe hanyarsu ta fita.

Daya daga cikin matakan da ake tunanin dauka shine a kyale su suyi ta zama a cikin kogon har sai ruwan da kansa ya kwarara, ya fice, abinda zai iya daukan tsawon wattani hudu daga yanzu.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG