Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Na Shirin Huce Fushinta Akan West Ham


'Yan wasan West Ham
'Yan wasan West Ham

Sai dai masu sharhi a fagen kwallon kafa na ganin, ita ma West Ham ba kanwar lasa ba ce, suna masu cewa, komai na iya faruwa a wasan.

Manchester United na shirin huce fushin kayen da ta sha a hannun Young Boys akan kungiyar West Ham United a gasar Premier League.

A ranar Talata Young Boys ta lallasa Manchester United da ci 2-1 a wasan farko na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai wato UEFA Champions League.

“Mun shirya maida martani ranar Lahadi.” Manchester United ta rubuta a shafinta na Twitter a ranar Laraba.

A ranar Lahadi West Ham za ta kara da Manchester United.

Gabanin ta wallafa wannan sako, kungiyar ta United ta kuma rubuta cewa, “mu tashi mu yunkuro a karshen makon nan.”

Sai dai masu sharhi a fagen kwallon kafa na ganin, ita ma West Ham ba kanwar lasa ba ce, suna masu cewa, komai na iya faruwa a wasan.

Manchester United ita ce a saman teburin gasar ta Premier bayan da ta kai Newcastle ta baro da ci 4-1 a karshen makon da ya gabata.

West Ham kuma na matsayi na takwasa da maki 8 a teburin na EPL.

A farkon wannan kakar wasa kungiyar ta yi cefanen manyan ‘yan wasa ciki har da Cristiano Ronaldo da ya yi kome.

Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?

Ole Gunnar Solskjaer
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG