Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tantance Lafiyar ‘Yan Matan Dapchi Da Aka Ceto


Garin Dapchi
Garin Dapchi

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatarwa da Muryar Amurka cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun sako ‘yan matan Dapchi yau Laraba, amma kungiyar Amnesty International ta jaddada cewa dole sai an gudanar da bincike.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, yanzu haka jami’an tsaro suna ta kokarin ganin sun tattara ‘yan matan guri guda domin a tantance lafiyarsu.

Fadar shugaban kasar dai bata bayar da wani cikakken bayani ba kan yadda aka samu ceto ‘yan matan ba.

Duk da yake dai gwamnati bata bayar da bayani kan cewa yadda aka kubutar da ‘yan matan ba, masana tsaro na ganin cewa dole ne a yi taka tsan-tsan.

Dakta Kabiru ‘Dan Ladi Lawanti, na jami’ar Ahmadu Bello na ganin cewa sako ‘yan matan abu ne mai kyau, amma kuma hatsarin dake tattare da hakan shine idan har gwamnati ta biya kudi ne aka saki ‘yan matan, hakan zai jefa sauran yara ‘yan makaranta cikin hatsari.

Sai dai kuma kungiyar Amnesty International ta ce tana farin cikin ganin an sako ‘yan matan, amma kuma tana nan kan bakanta na ganin an gudanar da bincike kan yadda tun farko aka sace ‘yan matan.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG