Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Taro Akan Mahimmancin Inganta Kwayoyin Halitta A Kano


Farfesa Hafiz Abubakar Mataimakin Gwamnan jihar Kano

A shekara ta 2014 ne, aka kafa cibiyar domin gudanar da ayyukan bincike da horas da dalibai a matakai daban daban kan fasahar da kimiyyar kwayoyin hallitun bil’adama da dabbobi da itatuwa da kuma tsirrai da dangoginsu.

Yau aka shiga rana ta biyu ta taron bita na yini hudu kan muhimman dabarun inganta kwayoyin hallittu a kimiyyance, wadda Cibiyar bincike kan kimiyyar sarrafa kwayoyin halittu ta Jami’ar Bayero Kano, wato Centre for Biotechnology Research, ta shirya.

Farfesa Auwalu Halliru Arzai dake zaman Daraktan Cibiyar, ya yi karin haske dangane da aikace aikacen ta da kuma alkibilar taron bitar irinsa na farko da suka shirya. Farfessa Arzai yace suna bincike ne akan kwayoyin halittu irinsu tsirrai da dabbobi da tsuntsaye da bishiyoyi domin a samar da kayayyakin da zasu anfani dan Adam. Alkiblar taron a cewarsa itace ta koyas da masana kimiya da fasaha sabbin dabaru na zamani kan bincike a fuskar noma, kiwon lafiya, inganta muhalli, inganta tsaro da binciken ayyukan laifuka ta hanyoyin zamani

Shi ko Farfesa Muhammad Yalwa Gwarzo, daya daga cikin masana ilimin kimiyyar kwayoyin hallitu wato Biotechnology, ya bayyana muhimmancin rungumar wannan sigar ilimi domin habaka abinci da magunguna da sauran muhimman ababen bukatun rayuwar bil’ada a najeriya. Ya ce shekaru hamsin da suka gabata yawan al'ummar Najeriya mutum miliyan sittin da shida ne amma yanzu ana da mutane miliyan 180 duk da cewa fadin kasar bai karu ba. Idan ba'a kawo wannan sani ba ko kasar da dinga sayen abinci ko kuma a mutu da yunwa. Wajibi ne a rungumi sabbin hanyoyi ta yadda kadadar dake bada buhun hatsi biyar da can yanzu yakamata ta bada ishirin ko talatin

Mataimakin gwamnan Kano Farfesa Hafiz Abubakar da wanda mashawarcin sa kan lamuran ilimi mai zurfi Dr Bakari Ado Hussain ya wakilta ya ce gwamnatin Kano bisa hadin gwiwa da ofishin jakadancin kasar Faransa na horas da wasu malamai dake koyar da darusan kimiyya a manyan makarantun Kano.

A ranar Alhamis mai zuwa ne za’a kammala taron bitar wadda masana ilimin kimiyya daga jami’o’I da kwalejojin fasaha dana ilmi da kuma cibiyoyin bincike daga sassan najeriya ke halarta.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG