Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Taro akan Sharuddan Ficewar Birtaniya Daga Kungiyar Tarayyar Turai


Austria EU Summit
Austria EU Summit

Shuwagabannin Kungiyar tarayyar turai sun fara tattaunawa akan sharuddan ficewar kasar Britaniya daga kungiyar tarayyar turai.

Shuwagabbani kungiyar tarayyar Turai sun taru a Salzburg, kasar Austria domin tattaunawa akan wasu muhimman batutuwa, wanda suka hada da ka’idodin ficewar burtaniya daga kungiyar tarayyar turai.


Yayin da Gwamnati mai ra’ayin rikau ta Britaniya ta rasa abubuwa da dama a dalilin ficewar ta, zata kuma fice daga harkokin kasuwancin tarayyar turai da kungiyar kostom.


A yanzu haka tana kokarin neman sausauci. Wata matsalar da ba’a magance ba itace makomar kan iyaka kasar Ireland wadda ke cikin kungiyar EU da kuma Ireland ta arewa ta Britaniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG