Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaben Shugaban Kasa a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika


Taswirar Kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Yan kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika na can suna kada kuri’unsu domin zaben shugaban kasar da ake yi a zagaye na biyu, tsakanin wasu tsoffin firai ministocin kasar biyu, a wani yunkuri na neman ma kasar zaman lafiya mai dorewa, bayan shekaru biyu da aka kwashe ana rikici.

Daga cikin ‘yan takarar akwai Anicet Goerges Dologuele, wanda ya lashe zaben a zagayen farko da aka yi a watan Disamba, inda ya samu kashi 24 na kuri’un da aka kada.

Sai kuma Faustin Archange Toudera wanda ya samu kashi 19 a zagayen na farko.

Baya ga wannan zabe na shugaban kasa, masu kada kuri’a har ila yau suna zaben ‘yan majalisu, bayan da wata babbar kotun kasar ta yi watsi da sakamakon zaben farko bisa dalilan cewa na tafka magudi.

Wadanda suka samu nasara a wadannan zabuka, su za su maye gurbin gwamnatin wucin gadi da aka kafa tun a shekarar 2014.

A shekarar 2013 mayakan Seleka suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize, lamarin da ya tsunduma kasar cikin rikicin da ta shiga, har ta kaiga ana fada tsakanin musulmi da kiristoci.

XS
SM
MD
LG