Accessibility links

Ana Zaman Dar-Dar A Garin Bama


Sojoji swun daure wani mai suna Bakura Ibrahim, mwanda suke zaton dan Boko Haram ne a jikin bishiya a Bama, talata 7 Mayu 2013

Hukumomi suka ce 'yan kungiyar Boko Haram su wajen 200 suka kai farmaki dauke da manyan bindigogi a kan garin na Bama, inda mutane 55 suka mutu.

An dauki matakan tsaro masu tsanani a garin Bama dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, a bayan da aka kashe mutane 55 a wasu hare-haren da 'yan kishin Islama dauke da muggan makamai suka kai kan wannan gari dake Jihar Borno.

Jami'an sojan Najeriya sun ce mutane 200 da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram, sun far ma garin na Baga dauke da manyan bindigogi da gurneti.

Wani kakakin rundunar sojoji yace 'yan bindigar sun kai farmaki a kan wani gidan kurkuku na tarayya, suka kashe ganduroba 14, suka kuma sako fursunoni 105. Har ila yau, sun kai farmaki a kan wani barikin soja, suka kona gine-ginen gwamnati da dama, ciki har da wani caji ofis na 'yan sanda da wani karamin asibiti.

Jami'ai suka ce an kashe sojoji akalla 2, da 'yan sanda 22, da fararen hula da dama, tare kuma da 'yan Boko Haram su 10.

An shirya gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno zai kai ziyara zuwa Bama a yau laraba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG