Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zanga Zangar Adawa Da Manufofin Taron G 20


Masu Zanga Zanga

A halin da ake ciki kuma, birnin Hamburg a kasar Jamus na fuskantar Karin zanga-zanga ta masu adawa da manufofin taron kolin kasashe masu karfin tattalin arziki da ake kammalawa yau asabar a birnin.

A bayan tarzomar da ta barke a sanadin zanga zangar a daren da ya shige zuwa asubahin yau asabar, ‘yan sandan Hamburg sun kama mutane akalla 13. Daga bisani kungiyar kare muhalli ta duniya da ake kira Greenpeace, ta rataye wani makeken allo a kan wata gadar dake kusa da wurin taron kolin, wanda a jiki aka rubuta cewa “Kungiyar G-20, ku kawo karshen amfani da kwal.”

Kafofin labarai sun ce ana sa ran za a gudanar da wata babbar zanga zanga a yau asabar da rana. Wata kungiya mai suna Hamburg Pushes Back ta ce tana sa ran mjutane dubu 30 zasu halarci wata zanga zangar da ta shirya a bakin ruwan Hamburg.

A jiya jumma’a, ‘yan zanga zanga sun yi mummunar arangama da ‘yan sanda, inda suka raunata ‘yan sanda kusan 200 da wasu ‘yan rajin masu yawa.

‘Yan sanda suka ce sun samo karin jami’ai 900 daga wasu sassan kasar domin su taimaka wajen shawo kan lamarin, abinda ya kawo adadin ‘yan sandan da aka girka a birnin Hamburg zuwa dubu 20 da dori.

‘Yan sandan sun yi sintirin wuraren da ake zanga zanga, kuma a yayin da akasarinsu ana yi ne cikin lumana, akwai wadanda suka sanya wuta a motoci, ko suka rika jifar ‘yan sanda da kiwalabe, ko suka yi kokarin shiga dakin da shugabannin suke yin taro.

Wasu ‘yan zanga zangar ma sun jefa bam na fetur, suka cinna wuta a kan tituna ko suka farfasa kantuna suna kwasar ganima.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG