Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Shugaban Kasar Brazil da Cin Hanci da Rashawa


Shugaban Brazil Michel Temer
Shugaban Brazil Michel Temer

A karon farko shugaban kasar Brazil Michael Temer yana fuskantar zargin cin hanci da rashawa kuma idan majalisar dokokin kasar ta amince zai fuskanci tuhuma a kotu lamarin da ka iya kaishi ga rabuwa da mukaminsa

A kasar Brazil babban mai shigar da kara ya shigar da wata kara yana zargin shugaban kasar na riko Michael Temer .

Ya zargi shugaban da cin hanci saboda ya karbi na goro daga shugaban wani kamfani mai sarafa nama. Akwai karin wasu zarge-zargen da nan gaba za’a gabatar dasu.

To sai dai bisa ga dokar kasar ana bukatar kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar kasar kafin a samu amincewa a hukumance a soma tuhumar shugaban kasar.

Mr. Temer shi ya gaji Dilma Rouseff shekara daya da ta gabata wadda aka tsige daga mulki saboda ta karya dokokin tsara kasafin kudin kasar.

Yawancin manyan ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa, yau kusan shekara daya ke nan ana bincikensu akan almundahana. Mr. Temer na iya zama shugaban kasar na farko da zai fuskanci tuhumar aikata babban laifi a tarihin kasar.

Wani tsohon shugaban kasar Brazil din Peter Hakin ya shaidawa Muryar Amurka cewa kokarin da Mr. Temer ya keyi domin ya samu karbuwa a idon jama’a tare da matakan tsuke aljihun gwamnati da ya dauka wanda ‘yan kasar suka ki amincewa dashi ka iya kawo masa cikas wajen fita daga zargin da ake masa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG