Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Sojojin Nijar Da Kashe Farar Hula Sama Da 100 Marasa Laifi


Wasu jojojin Nijar a Diffa
Wasu jojojin Nijar a Diffa

A Janhuriyar Nijar, ga dukkan alamu, bangaren tsaro zai sake shiga wata rigima bayan da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta zargi sojojin kasar da kare farar hula sama da 100 wadanda ba su aikata laifin komai ba.

A wani al’amari da ka iya janyo cece kuce da takaddama, jamhuriyar Nijar hukumar kare hakin dan adam ta CNDH ta fitar da rahotonta bayan wani binciken da ta gudanar a karkarar Inates da Ayorou da ke yankin Tilabery da nufin tantance gaskiyar lamari game da zargin dakarun kasar da hallaka farar hula sama da 100 ba tare da aikata lafin komai ba.

Tun a washegarin bayyanar labarin kashe kashen da ake zargin dakarun tsaron Nijar da aikatawa akan wasu farar hula kimanin 102 a karkarar Inates da Ayorou iyakar kasar da Mali ya sa Hukumar Kare Hakkin Dan Adam kaddamar da bincike a wadannan wurare domin tantance gaskiyar abin da ya faru. Bayan aiki na tsawon watanni 3, binciken na hukumar CNDH ya zakulo gawaki kimanin 71 da aka binne a ramuka 6 daga cikin 7 din da aka yi nasarar ganowa, abinda ke gaskata zargin da aka yi a can baya.

Flintlock 2017 builds trust in Niger
Flintlock 2017 builds trust in Niger

Almansour Mohamed na kungiyar CAPAAN na daga cikin ‘yan fafitikar da suka halarci taron baje wannan rahoto, kuma ya ce a ganinsa hukumar ta yi binciken da ya kamata kuma akwai alamomin da ke nuna cewa an ji raunuka ma mutanen musamman ma a kawunansu.

Sai dai ra’ayoyin jama’a sun sha bamban a game da sahihancin bayanan da hukumarrtace ta tattara a yayin gudanar da bincike. Shugaban kungyar hakkin dan adam ta CADDED Dambaji Son Allah y ace shi bisa ga abin da ya gani bai ta yakinin cewa sojojin Nijar sun tafka wannan ta’asar.

A cewar hukumar ta CNDH tuni ta damkawa shugaban kasa Issouhou Mahamadou wannan rahoto abinda ya wasu ke ganin ya kamata a bai wa alkalai wannan sakamakon binciken su dau matakin da ya dace na daukar matakan hukunta masu hannu a kashe kashen na Inates da Ayorou a matsayin matakin gaba. To amma wasun kuma na cewa ya zama wajibi a kara zurfafa bincike.

Flintlock 2017 builds trust in Niger
Flintlock 2017 builds trust in Niger

Shuwagabanin Jami’an tsaron da tawagar masu bincike ta tuntuba a yayin zagayenta sun ayyana wannan zargi na kashe kashe tamkar wata farfagandar da aka kitsa takanas da nufin daukar hankali jama’ar cikin gida da waje yayin da mazaunan karkara da abin ya faru ke cewa tabbas an yi wa danginsu kisan gilla da sunan yaki da ta’addanci to amma hukumar CNDH ta jaddada cewa ba ta da niyyar katsewa dakarun tsaro hanzarin aiki ta hanyar wannan bincike, illa kawai ta yi amfani ne da hurumin da kundin tsarin mulki ya ba ta a matsayinta na mai kare mutuncin Nijear a idon duniya akan maganar mutunta ‘yancin dan adam.

Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG