Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Angela Merkel Ta lashe Zabe Zagaye Na Hudu


NIGER: Angela Merkel ziyararta kasar Nijar
NIGER: Angela Merkel ziyararta kasar Nijar

Angela Merkel ta sake yin nasarar a zaben da aka gudanar a kasar dta Jamus.Wannan dai shine karo na 4 tana lashe zaben, wanda rabon da a samu wanda yayi wannan nasarar tun bayan yakin duniya na biyu

Shugabar Jamus Angela Merkel ta ci wa'adi na hudu a matsayin Shugabar kasar Jamus a zaben Shugaban kasa, wanda tun watanni uku da aka fara yakin neman zaben, alamomi su ka nuna yadda sakamakon zai kasance kenan. To amma jam'iyyarta ta Christian Democrat ta samu kuri'u kasa da yadda aka yi hasashe a yayin da kuma jam'iyyar masu rikon-rikau ta cilla, ta samu kuri'u fiye da yadda akasarin masu hasashe su ka yi.

Hasasoshin da aka fai yadda da su, waddan da alkalumansu su ka dogara ga bayanan da su ka biyo bayan dab da kammala zaben, na nuna jam'iyyarsu Merkel mai mulki ta Christian Democratic Union da mai dasawa da ita na yankin Bavarian mai suna Christian Social Union, sun samu kimamnin kashi 32.5% na kuri'un; wanda hakan zai sa ta zama Shugabar Jamus ta farko da ta ci wa'adi na hudu tun bayan yakin duniya na biyu.

Da masu hasashe sun yi kiyasin cewa gamayyar ta su Merkel ta jam'iyyun na CDU da CSU za ta ci kashi 36% zuwa 39% na kuri'un.

Ganin yadda gamayyar ta CDU ta samu kasa da yadda aka yi hasashe da kuma yadda jam'iyyar 'yan rikon rikau ta samu kuri'u fiye da yadda aka yi hasashe, ace nasarar ta Merkel tamkar wata zuma ce mai daci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG