Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anya Kuwa Rundunar Zaman Lafiya Dole Sun San Inda Aka Ajiye Yan Matan Chibok?


Masu Zanga-Zanga sun bukaci Gwamnati dasu kubuto da 'yan matan Chibok da aka sace, 14 ga Oktoba 2014.

Cikin watan Maris ne a cibiyar yaki da Boko Haram dake Maiduguri, kwamandan rudunar Zaman Lafiya Dole, Manjo Janar Leo Irabor, ya bayar da kwarin gwiwar karya lagon ‘yan ta’adda da nuna cewa za a kawo karshensu nan bada dadewa ba.

To sai dai kuma jaridar Daily Independent ta rawaito Irabor na cewa matan nan na Chibok na dajin Sambisa, kuma jami’ansa na matsawa can don kwato su ko ceto su, wasunsu kuma a cewar rahotan na dab da kan iyakar Nijar da Chadi, banda wannnan dai babu wani karin bayani daga kafar rundunar soja.

A cewar masana harkar tsaro na cewa Irabor dai na magana ne irin ta bayar da kwarin gwiwa kawai, don hankalin mutane da iyayen matan ya kwanta.

Masani kan harkar yan ta’adda Dakta Mohammed Bello na jami’ar jigawa na tababar labarin, inda yace wannan harsashe ne domin kuwa ba zai iya fadin inda aka ajiye wadannan mata ba, kuma babu yarda za a yi a jiye mata 200 a guri guda ba abune mai yiwuwa ba.

Ganin faifan bidiyo na wasu daga cikin matan a tabijin na CNN, na nunin suna raye koda ana kokwanton wasunsu basa rayen, idan ba a manta ba Irabor ya karbi aikin kwamanda daga manjo janar Hassan Umaru, wanda ya koma hedikwatar sojoji a Abuja, kuma kwamandan da suka gada janar Yusha’u Abubakar ya rasu sakamakon hadarin mota kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG