Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Amfani Da Makami mai Guba A Gabashin Mosul


Mai kula da al’amuran da suka shafi kare hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Iraqi ya gabatar da gargadin yiwuwar anyi amfani da makami mai guba a Mosul

Anyi amfani da makami mai guban ne a inda Mayakan ISIS suke yaki da Dakarun Iraqi da Amurka ke marawa baya.

Lisa Grande wacce tayi kira da ayi bincike akan al'amarin tace “ Wannan abune mai muni” ta yi kira da cewa idan dai har wannan al’amari ya tabbata “Karya dokar hakkin Dan Adam ta kasa da kasa ne Mai muni da kuma laifin yaki, kowane ne akai amfani da makamin akansu.”

Kwamitin Kasa da kasa na kungiyar Red Cross yace an kai mutane bakwai asibiti kusa da Mosul ana yi musu magani dangane da sinadari da ya shafesu.

Daraktan Yankin na Kungiyar Red Cross a gabas ta tsakiya Robert Mardini yace yara biyar da kuma mata biyu ake dubawa a asibiti “wadanda suka nuna alamun kuna ta sinadari a jikinsu,” Alamun sun hada da Kuna da Jan ido da zugi da Amai gami da Tari.

Mardini ya kara da cewa, “Amfani da makami mai guba haramun ne karkashin dokar kasa da kasa ta kare hakkin dan Adam. Mun damu kwarai da irin abinda abokanan aikin mu suka gani kuma sunyi Allah wadai da amfani da duk wani makami mai guba daga ko wanne bangare dake yakin.”

Harin da ake zargi ya faru ne a satin da ya gabata a gabashin Mosul.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG