Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Nasarar Hallaka Wasu Masu Kame Mutane Suna Garkuwa Dasu


KANO: Masu sace mutane da 'yansandan Kano suka cafke a dajin Falgore

Anyi nasarar kame wasu mutane masu garkuwa da mutane tare da hallaka su a cikin jihgar Taraba, Mutanen da aka kashe an same su da bindigogi da wasu muggan makamai kuma kafin mutuwar su sun bada tabbacin cewa ba shakka suna aikata wannan danyen aikin

Rundunan yan sandan jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da kissan wasu matasa da suka addabi jama’a wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar Matasa da suka harzuka ne suka kashe wasu samari guda hudu da ake zargi masu satan mutane ne su yi garkuwa da su,kuma lamarin ya faru a kauyen Tella a karamar hukumar Gassol na jihar Taraba.

Bayanai sun nuna cewa wadanda aka kashen sun dade suna addabar mazauna garin na Tella da fashi da kuma garkuwa da mutane kafin su fada ragar yan sakai na yan banga.

Hakan kuma rahotanni sun bayyana cewa an samu bindiga da wasu makamai a hannun wadanda aka kashen, kuma sun shaida wa wadanda suka kama su cewa iyayen gidansu na cikin daji wadansu kuma na cikin garin Jalingo.

Kakakin rundunan yan sandan jihar Taraban David Misal ya tabbatar da aukuwan lamarin tare da gargadin jama’a da su daina daukan doka a hannu.

Haka nan kuma, Baya ma dai ga wadanda aka kashen haka nan kuma jami’an tsaro sun cafke daya daga cikin masu wannan tu’annuti, da akewa lakabi da Kinko da ya sha da kyar .

Daga bara zuwa bana an sace sama da mutum 64 a kananan hukumomin Gassol da Bali, inda bayanai suka ce an biya sama da Naira miliyan 100 kudin fansa kafin sako su.

Ga Ibrahim Abdul Azeez da Karin Bayani 4’09

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG