Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yiwa karin jam’iyun siyasa guda 5 rajista a Nigeria


Muritala Diekola, display his new voters registration card in Lagos, Nigeria, Saturday, Jan. 15, 2011. An effort to register 70 million voters across Nigeria before its April presidential election wobbled to a start Saturday, as volunteers fought with mal
Muritala Diekola, display his new voters registration card in Lagos, Nigeria, Saturday, Jan. 15, 2011. An effort to register 70 million voters across Nigeria before its April presidential election wobbled to a start Saturday, as volunteers fought with mal

Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta mika wa sabbin jamiyyu 5 takardan shedan rajista a wani taron da aka gudanar a heduikwatar hukumar dake Abuja.

Jamiyyun ko sun hada da Action Democratic Party, (ADP) All Democratic Movement(ADM), da Advance Peoples Alliance (APA), da New Generation Party of Nigeria (NGM), sai kuma Young Progress Party (YPP).

Shugaban hukumar Zaben Farfesa Mamud Yakubu ya bukaci jamiyyun su baiwa kowa damar a dama dashi cikin jamiyyun, kana su guje wa tabiaar ko a mutu ko ayi rai a lamurran zabe ko siyasa.

Farfesa Yakubu yace, ’Jamaa ke zabar shugabannin ta hanyar jamiyyun siyasa , don haka menene amfanin hayaniya, ayi ta fada ayi ta buge-buge. Siyasa ka fadi raayin ka ne wannan ya fadi nasa.

Yakubu Shamdam shine shugaban sabuwar jamiyyar Matasa YPP.

Yace Mun gaji da yadda abubbuwa a jamiyyu ke faruwa a kasar nan, abinda manyan kasar nan keyi daga 1960 har zuwa yau, har yanzu matasan mu suna wahala, shi yasa muka kawo wannan jamiyyar’’

Shi kuma shugaban jam’iyar ADP Injiniya Yabagi Yusuf Sani, yace Kasar nan tana cikin wani hali na Lahaula Walakuwata, amma abinda ya janyo haka shine gwamnatin dake kan mulki bata san yadda zata tafiyar da harkokin gwamnati ba, abu ne kamar an haukace’’

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG