Accessibility links

Anyi zanga zangar a harabar kotun kolin Amirka

  • Jummai Ali

Wani mai zanga zanga a harabar kotun kolin Amirka

Batun kiwon lafiya yasa masu zanga zanga zuwa matakalar kotun koli. Masu zanga zangar sun kunshi masu goyon da kuma wadanda basu goyon bayan wannan doka. A wasu lokutan akan yi muhawarar ba zata ta tada jijiyoyin wuya tsakanin bangarorin biyu, to amma ana yi cikin lumana da sanin ya kamata. Ed Hale yana daya daga cikin masu goyon bayan wannan doka ta yiwa tsarin kiwon lafiya kwaskwarima. Yace abinda takaici ne cewa an zatar da wannan doka a lokacinda aka shiga mawuyacin hali, wato lokacinda aka yi fama da mugun komadar tattalin arziki. To amma anyi shekaru dari ana fafitukar ko kuma gwagwarmayar ganin an zartar da irin wannan doka, lokaci yayi daya kamata a zartar. Lokaci yayi daya kamata Amirka tabi sahun sauran kasashen duniya. Sai kuma wata mace mai suna Daveta sanye da rigar wata kungiyar jama’a. Itama tana goyon bayan wannan doka, domin miliyoyin jama’a wadanda ba zasu iya ko kuma basu da halin samun inshore na kiwon lafiya ba zasu samu, a ganinta kowa yana bukatar kiwon lafiya. Wannan batu ba kawai na wadanda suke da inshore bane a’a batu ne na wadanda basu da inshra. Tace tazo ne domin ita tana da inshore amma kuma tazo ne domin wadanda basu da inshore. To amma kuma akwai masu zanga zanga da dama wadanda basa goyon bayan wannan doka, ciki harda wani mutum mai suna Ken Campbell, wani likitan hakori daga jihar California. Yace shi baya goyon bayan bangaren dokar daya tanadi kowa sai ya samu inshore kan shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, ko kuma ya biya tara.

Yace wadanda ke zaune anan Washington suna yanke shawarar akan abubuwa, basu ma san dashi ko iyalisa ba. Basu san sunayen ‘ya’yansa ba. A saboda haka yace, basu da yanci gaya wa iyalinsa abinda suke bukatar saye da abinda suke bukata ba. A saboda haka su kyale shi ya gudanar da rayuwarsa yadda nake so. Ita ma Amy Brighton, wata mace daga Ohio bata goyon bayan wannan doka ta Obama

Tace wannan doka a yadda take ta sabawa tsarin mulkin kasa. Tace ba wai basu goyon bayan a yiwa tsarin kiwon lafiya kwaskwarima bane. A’a su dai wannan doka ce basu yarda da it aba. Cikin dai kwanaki uku Kotu kolin Ammirka zata saurari hujojin sa’o’i biyar da rabi. Ko ma dai yaya kotun kolin ta yanke hukunci kan karshen watan Yuni, hukuncin data yanke zai dora tasiri sosai ga zaben shugaban kasar da za’a yi a bana.

XS
SM
MD
LG