Accessibility links

Kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa zasu kafa bankin raya kasa

  • Jummai Ali

Shugabanin a wajen taron kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da aka yi a Indiya.

Kasashen Brazil da Rasha da China da Indiya da kuma Afrika ta kudu wadanda tattalin arzikinsu ke bunkasa su kamalla taro a Indiya.

Manyan kasashe biyar, wadanda tattalin arzikinsu ke bunkasa da suka hada da kasar Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afrika ta kudu sun kamalla taron kolinsu a New Delhi baban birnin kasar Indiya, jiya Alhamis tare da yin kiran kafa bankin raya kasa na hadin gwiwa.

Shugabanin kasashe biyar din wadanda ake cewa BRICS a takaice, sunce suna bukatar karin wakilici a tsari ko kuma harkokin kudin kasa da kasa.

Prime Ministan Indiya Manmohan Singh wanda ya karbi bakoncin taron kolin na wuni guda, yace kasashen suna kusantar daukan wani muhimmin matakin inganta zuba jarin da zai taimakesu, wato kafa bankin raya kasa na hadin gwiwa wanda kasashen na BRICS da sauran kasashe masu tasowa zasu dauki dawainiyar gudanarwa.

Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma yace shi da sauran shugabanin kasashen Afrika sunyi maraba da yunkurin kafa wannan banki, yana mai fadin cewa kafa bankin, yana da kafar taimakawa wajen samar da aiyuka yin masu kyau a kasashe masu tasowa.

Takwaran aikinsa na Rasha kuma, Dmitry Medvedev yace kasashen BRICS zasu taka muhimmiyar rawa wajen yiwa yadda ake gudanar da mulkin duniya kwaskwarima a yan shekaru masu zuwa.

XS
SM
MD
LG