Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC A Jihar Nasarawa Ta Fara Daukar Matakan Sasanta Yan Majalisun Jihar


APC

Jam’iyyar APC a jihar Nasarawa tace ta fara daukan matakan sasanta bangarori biyu na majalisar dokokin jihar, bayan wata hatsaniya da ta kai ga baiwa hammata iska a majalisar.

Majalisar dokokin dai ta samu baraka ne bayan da wasu yan majalisar 17 suka halarci gayyatar da gwamnan jihar yayi musu, kan matakin da ya dauka na nada kantomomi a kananan hukumomin jihar, yayin da wasu yan majalisar guda 6 suka nuna adawa da matakin.

A cewar sakataren jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello, a matsayinsu na iyaye suna kan tattaunawa da yan majalisar don sasanta su. Inda ya kara da cewa zasu duba suga waye ke da laifi su kuma gaya masa laifinsa, da kuma tabbatar da hakan bai sake faruwa ba nan gaba.

A jiya ne bangaren yan majalisar dake goyon bayan matakin gwamna na nada kantomomin, suka gudanar da taron manema labarai don fayyace matsayinsu na dakatar da yan majalisar 6 da suka bijirewa matakin na gwamna.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG