Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin APC Na Fuskantar Barazanar Bangarewa Ne?


Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa ta Sake Neman Wa'adin Shugabanci
Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa ta Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Ga dukkan alamu, barakar da ta kunno kai a jam'iyya mai mulki ta APC a wasu jihohin Najeriya na kara fadada, tun bayan zaben mazabu da aka gudanar a kasar, yayin da masharhanta ke gargadin cewa hakan ka iya sa wankin hula ya kai jam'iyyar dare.

Bayanai daga Najeriya na kara nuni da cewa ana ci gaba da samun baraka a wasu daga cikin jihohin da jam’iyyar APC ke jagoranta, tun bayan da aka kammala zaben mazabu a duk fadin kasar.

Jaridar Daily Trust a shafinta na yanar gizo a yau Lahadi ta ruwaito cewa an samu baraka a jihohin Kwara, Oyo, Kogi, Kano baya ga wasu jihohi.

Zabukan har ila yau, sun haifar da sabani a jihar Imo inda gwamnan jihar Rochas Okorocha ya kalaubalanci sakamakon zaben.

Masu lura da al’amura na ganin wannan matsala da jam’iyyar ke fuskanta a kusan daukacin kasar ka iya zama mata kalubale, lura da cewa ana tunkarar zaben gama gari a shekara mai zuwa.

Rahotanni sun ce tuni aka samu bangarewa a wasu jihohi a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar, misali jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jam’iyyar ta bangare zuwa gida biyu a jihar Kwara.

Akwai bangaren da shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki yake jagoranta, yayin da Ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammed, ke jagorantar daya bangaren.

Haka ma lamarin yake a jihar Kogi, inda jam’iyyar ta bangare biyu acewar jaridar.

Babban Sakataren jam’iyyar ta APC, Mai Mala Buni, a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a makon da ya gabata, ya ce akwai kwamitin shigar da korafi da jam’iyyar ta kafa a kowacce jiha.

Ya yi kira ga daukacin masu korafi da su garzaya zuwa wadannan kwamitoci domin gabatar da korafe-korafensu.

Haka zalika, wasu manyan jami'an jam'iyyar da Muryar Amurka ta zanta da su, sun ce irin wannan rikici ba sabon abu ba ne, kuma za su sasanta kansu komin dadewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG