Accessibility links

Bayan kwana goma da kammala zaben fitar da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kaduna har yanzu jam'iyyar bata iya bayyana sakamakon ba

Kawo yanzu kwamitin kula da zaben shugabannin mazabun jam'iyyar APC na jihar Kaduna ya kasa bayyana sunayen wadanda suka lashe zaben da aka yi kimanin kwanaki goma da suka gabata.

Tuni dai a wasu jihohin Najeriya aka kammala zaben shugabannin jam'iyyar yanzu jiran zaben shugabannin jam'iyyar na kasa suke yi. To amma a jihar Kaduna ko na kananan hukumomi ma ba'a san sakamako ba balantana su soma tunanin na kasa gaba daya. Yanzu dai 'yan jam'iyyar a jihar Kaduna suna tambaya shin yaushe ne zasu ji sakamakon zabukan da suka yi.

Dr Hakeem Baba Ahmed shugaban jam'iyyar na riko a jihar Kaduna yace ko su ma tambayar da su keyi ke nan bayan kwana goma da kammala zabukan. Babu wasu bayanai akan wadanda suka ci nasara da wadanda suka fadi da kuma wuraren da watakila suna da matsala kuma ana bukatar a sake zaben. Yace hankalinsu ya tashi. Sun matsu, jam'arsu ma sun matsu. Sun tuntubi kwamitin da ya gudanar da zabukan amma babu wani takamaiman bayani.

Amma sakataren kwamitin Barrister Mahmud yace kwamitin kula da zaben yana nan yana aiki tukuru domin warware sarkakiyar da ta kawo cikas ga zaben da yace za'a fadi wadan da suka lashe kuma a wasu mazaban za'a sake zabe. Yace suna kokarin su tantance sakamakon zabukan da aka yi. Yace sun kusa kammala tantance sakamakon. Yace abun da ya kawo cikas shi ne wadanda ko takardar tsayawa takara basu saya ba sai gashi sunayensu sun bayyana a zabukan. Irin wadannan sun gurbata sunayen wadanda yakamata su yi takara. Yace sunayen wadanda suka kaiwa INEC yakamata su ne zasu tsaya takara. Da zara sun gama zasu bayyana sakamakon zaben.

Barrister Mahmud yace idan wanda bai sayi takardar tsayawa takara ba amma kuma sunansa ya fito cewa ya ci dole su soke sunansa domin idan suka bayyana sunan to gyrawa zai yi wuya. Irin matsalolin da suke fuskanta ke nan. Sabili da haka akwai wuraren da yakamata a sake zabe kafin ma su yi na kananan hukumomi.

Zaben na APC ya tayarda wasu korafe-korafe da dama. Hajiya Hafsat Mohammed Baba tace basu ji dadi ba yadda wasu suka hana a yi zabuka a wasu gundumomi har ma an jikata wani wanda yanzu yana kwance a asibiti. Sun rubutawa uwar jam'iyya ta san matakan da zata dauka domin wasu yaran da aka kama sun fadi sunayen wadanda suka aikosu. Hajiya tace suna fata za'a soke zabe a duk inda aka tada hankali a sake wani zaben domin a baiwa mutane daman zaban wanda suke so

To saidai wani jigon jam'iyyar a jihar Kaduna Alhaji Mamadi Abubakar yace zaben yayi kyau. Yace shi bai taba ganin zaben da yayi daidai ba kaman wanda aka gudanar ba.

Ga rahoton Isah Lawal Ikara.
XS
SM
MD
LG