Accessibility links

Tsintsiyar APC na cigaba da share 'ya'yan PDP daga kujerunsu yayin da ta share 27 daga majalisar dokokin Sokoto cikin 30. Uku kawai ne tsintsiyar bata kai kansu ba tukunna.

Da alama tsinitsiyar APC sai cigaba ta keyi tana share 'yan jam'iyyar PDP daga kujerunsu ko na tarayya ko na jihohi.

Sharar tsintsiyar APC ta kai jihar Sokoto inda kakakin majalisar dokokin Lawal Mohammed Zayyana ya jagoranci 'yan majalisar 26 zuwa fadar gwamnatin jihar inda suka nunawa gwamnan jihar Wamako niyarsu ta barin jam'iyyar PDP zuwa APC.

'Yan majalisar 27 daga cikin 30 sun yanke shawarar bin gwamnan ne wanda tuni tare da wasu gwamnoni hudu suka canza sheka zuwa APC.

Kakakin majalisar Zayyana ya ce a mazabunsu mutane sun nuna cewa suna goyon bayan tafiya da APC tun da kuma suna wakiltar jama'a ne duk abun da suke so zasu yi. Saboda haka suka ga yakamata su kawo karshen kasancewa cikin PDP su nuna sun yadda a yi wannan tafiya tare da su.

Dangane da sauran ukun da basu shiga APC ba kakakin ya ce wanan ra'ayi ne kawai kuma watakila kafin su yi nisa su ma suna iya su kasance tare da su. Kan cewa duk wanda ya canza sheka zai rasa kujerarsa kakakin ya ce doka tana nan kuma kotu ta san abun da doka ta ce domin haka su basu damu ba.

A jawabinsa gwamna Wamako ya ce rashin shugabanci na gari ya sa PDP ke rasa 'ya'yanta. Ya kuma yiwa hannunka mai sanda a kan bita da kuli da PDP ke shirin yiwa wadanda suka canza sheka. Gwamnan ya tunashe da PDP lokacin da wasu gwamnoni suka bar jam'iyyunsu suka shiga PDP murna ta dinga yi. Yanzu da ta yi asarar nata ta tafi kotu amma ya yi mamaki ko dokokin biyu ne yanzu.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG