Accessibility links

Bamanga Tukur ya Musanta Shirin Ficewar David Mark da Aminu Tambuwal Daga PDP


Hira da Shugaban Jam'iyyar PDP na Nigeria.

Siyarsa Najeriya sai canza salo ta keyi tun lokacin da wasu gwamnoni da 'yan majalisu suka fice daga jam'iyyar PDP mai mulki zuwa ta adawa APC

A firar da abokin aiki Alhaji Aliyu Mustapha ya yi da shugaban PDP mai mulkin Najeriya Alhaji Bamanga Tukur, tamkar babu abun da ya girgiza jam'iyyarsu.

Da aka tambayi Bamanga Tukur ko David Mark da Aminu Tambuwal suna shirin barin jam'iyyar PDP sai ya fashe da dariya. Ya ce ta yaya za'a yi tsammani David Marka wanda jam'iyyarsa ta bashi mukami zai barta ya shiga wata jam'iyya. Ya ce duk maganganun banza ne kawai. Ya ce wadanda suka fita ba bi da hankali ba ne. Yaya za'a ce wanda ya zama gwamna a karkashin jam'iyya ta kuma bashi duk abubuwan da suka kamata a ce ya koma wata jam'iyyar.

Idan Bamanga Tukur bashi da shakka kan David Mark to Aminu Tambuwal kuma fa? Sai ya ce shi bashi da shakka domin dukansu basu gaya masa cewa suna shirin barin jam'iyyarsu. Kafin ya yi tafiya zuwa Amurka sun yi taro da manyan PDP da suka hada da Aminu Tambuwal da David Mark dangane da yadda zasu bunkasa jam'iyyarsu. Ya ce wajen su dari da hamsin suka yi taron. Babu wani daga cikinsu da ya ce zai fice.

Da aka fada masa cewa Kano da Sokoto da Adamawa sun fice daga PDP sai ya ce gwamnoninsu ne suka tafi. Gwamnonin da suka tafi basu tafi da jama'arsu ba domin basu tara jama'asu sun gaya masu sun fice daga PDP ba. Da aka ce idan gwamnoni sun fita suna fita da kwamishanoni sai ya ce ai su gwamnonin suka nada kwamishanonin.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG