Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta Yi Taron Bayyana Manufofinta a Abuja


APC
APC

Yayin da zaben shekarar 2015 ke kara karatowa , jam'iyyar adawa ta APC ta yi taron bayyanawa jama'ar Najeriya manufofinta na siyasa a Abuja.

Kamar yadda ta sanar da farkon wannan makon jam'iyyar adawa ta APC ta gudanar da taron bayyanawa 'yan Najeriya manufofinta.

Bayan jawaban manyan shugabannin jam'iyyar a Abuja taron ya kasance cikin murna da annashuwa. An gabatarda jawabai daban daban amma wanda ya fi daukan hankali shi ne na tsohuwar ministar ilimi a lokacin mulkin Chief Olusegun Obasanjo Madam Obi Ezekiesili. Tsohuwar ministar tace al'umman Najeriya suna bukatan 'yansiyasa masu kwazo da halaye nagari da kuma kwarewa a sanin makaman aiki. Ta kara da cewa wadannan abubuwa uku yakamata ku manlaka kafin ku soma tunanin son jan ragamar mulkin kasar domin kaita hawan tudun natsira.

Gwamnonin jam'iyyar su goma sha shida suka bayyana manufofin daya bayan daya a wani salo na daban da ya zama kamar bude sabon babi a siyasar kasar gabanin zabe mai zuwa kamar yadda Sanata Alkali Jajere ya bayyana. Yace sun gabatarda manufofinsu ga 'yan Najeriya da nufin cetosu daga halin kakanikayi da suka shiga. Akwai tabarbarewar tsaro da lalacewar zamantakewa da rashin aikin yi da tabarbarewar ilimi da aikin kiwon lafiya da aikin gona har ma da hanyoyin kasar.

Sanata Jajere ya kara da cewa kasar Najeriya an dagargazata kuma dole ne a samu 'yan kishin kasa wadanda zasu tallafa domin a mayarda kasar kan turbar cigaba cikn lumana.

Dangane da alkawarin da jam'iyyar tayi na kawar da cin hanci da rashawa wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta tambayi Sanatan yadda zasu cimma wannan manufa ganin cewa wasu daga PDP sun shiga jam'iyyarsu. Yace Janaral Buhari shi ne shugaban jam'iyyar kuma babu wani dan Najeriya da zai ce Buhari zai yadda da cin hanci da rashawa, ko da hadin bakinsa ko kuma da saninsa. Duk inda yayi shugabanci an gani. Bai aikata wani abun asha ba.

A wani abu kamar mayarda martani mai magana da yawun PDP Olisa Metuh yace sun duba sun gani manufofin jam'iyyar APC a rubuce amma bai yi bayanin komi ba kan cigaban kasar.
XS
SM
MD
LG