Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dogayan Layuka a Gidajen Mai a Jihar Sakwaton a Arewacin Najeriya


Diezani Allison-Madueke ministar albarkatun man fetur ta Najeriya.

Rashin wadatatcen man fetur a adabi mutanen jihar sakwato

Karancin man fetur ya adabi jihar Sakwato a arewacin Najeriya,inda gidan man NNPC da kuma kalilan daga cikin gidajen man yan kasuwa ne suke sayarda man akan farashin da gwamnati ta kayyade.

Daruruwan mutane ne suke cikin layuka da hayaniya da gwagwarmaya harda ba hammata iska saboda son siyar man fetur, neman haka yasa wasu daga cikin mutane kwana a layin gidajen man suka yi.

Jama'a na kokawa domin wahalar da ake sha domin rashin wadatatcen mai wanda yakasance abokin aiki.

Kawo yanzu dai babu wanda zai bada takamaiman dalilin da yasa ake samun karancin man fetur a kasar daidai wannan lokacin. Wannan lamarin haka yake a Legas da Kano balantana ma cikin karkara inda dama can basa samun isasshen man.

Karancin man da a keyi ya takurawa rayuwar al'umma na yau da kullum yayin da wadanda abun ya rataya a kansu sun yi shiru kamar an shuka dusa.

Ga rahoton da ya kara bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG