Accessibility links

APC Tana Zargin Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Danjuma Goje da Haddasa Rikicinda Jam'iyyar Take Fama da Shi a jihar Gombe

  • Aliyu Imam

APC

Wani jigon jam'iyyar ta kasa keftin Bala Jibrin ne yayi wannan zargi lokacinda yake zantawa da manema labarai a Bauci.

Jam'iyyar APC mai hamayya a Najeriya tana zargin tsohon gwamnan jihar Gombe Mohammed Danjuma Goje, da zama ummul khabaisin rikicinda jam'iyyar take fama da shi a cikin jihar.

Mukaddashin ma'ajin jam'iyyar na kasa keftin Bala Jibrin wanda ya bayyana haka ga manema labarai yace Goje tsohon gwamna ne saboda haka damar da aka baiwa gwamnoni da suke mulki shi ba zai samu ba. Damar da aka bashi shine fidda shugaba daya, amma ba zai handamae dukkan mukamai ba.

Jibrin ya kuma aza laifin haka kan shugaban jam'iyyar na shiyya Adamu Duhu wand a da yardarsa ne senata Danjuma Goje yake yadda ya ga dama

XS
SM
MD
LG