Accessibility links

Mazabar Danjuma Goje Bata Amince da Canza Shekar da Ya Yi ba


Senator Danjuma Goje tsohon gwamnan jihar Gombe

Kasa da mako guda bayan ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC sai gashi Danjuma Goje na fuskantar fushin mazabarsa domin jama'arsa sun ce basu amince da abun da ya yi ba.

Tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje ya shiga hali mai sarkakiya da mazabarsa.

Bisa ga alamu murna na son komawa ciki ga tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje wanda yanzu sanato ne a majalisar dattawan Najeriya domin mazabarsa ta yi watsi da canza shekar da ya yi zuwa jam'iyyar APC. Bello Mohammed daga mazabar ya ce gashin kansa ya yi. Ya ce nan da mako biyu zasu samu duk adadin sa hannun mutane da doka ta tana domin su janyeshi daga majalisar dattawan Najeriya. Ya ce lauyoyi suna nan suna basu shawara.

Haka ma APC reshen jihar Gombe na nuna adawa da kasancewar Danjuma Goje a cikinsu. Kakakin hadakar jam'iyyun na jihar Gombe Ibrahim Waziri ya shaidawa manema labarai a karshen taron jam'iyyarsu. Ya ce akwai takaddama sabili da damar da uwar jam'iyyar ta baiwa Danjuma Goje ya zama shugabanta a jihar ta Gombe. Ya ce sai suka wayi gari sai ga Goje ya zo zai kafa shugabancin jam'iyyar daga bangarensa na sabuwar PDP lamarin da su basu amince da shi ba.

Mai magana da yawun Danjuma Goje Sani Adamu ya ce sanaton bai canza sheka ba sai da ya shaidawa mazabarsa.

XS
SM
MD
LG