Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taron Ta Na Kasa A Watan Gobe


Wasu gwamnonin jam'iyyar APC(Facebook/APC)

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta gudanar da babban taron ta na zabar shugabanni a watan gobe wato febreru.

Wannan sanarwar ta biyo bayan taron gwamnonin jam’iyyar ce a Abuja da ya samu halartar akasarin gwamnonin.

Shugaban kungiyar gwamnonin na APC gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ba da tabbacin bayan kammala taron, amma bai tantance ko bayyana hakikanin ranar da za a gudanar da taron ba.

Gabanin wannan sanarwa an samu raderadin dage babban taron zuwa watan yuni na bana.

Babban taron dai zai zama zakaran gwajin dafi ga hadin kan APC don tinkarar babban zaben 2023 a yayin da a ke samun rabuwar kawuna a tsakanin jagororin jam’iyyar a matakin jihohi.


Manyan ‘yan jam’iyyar da akasari tsoffin gwamnoni ne, sun fito fili suna neman shugabancin jam’iyyar.

Tsoffin gwamnonin da ke neman shugabancin jam'iyar sun hada da Ali Modu Sheriff, Tanko Almakura, Abdul’aziz Yari da sauran su.


Taron ya nuna mara baya ga shugaba Buhari da kuma shugaban kwamitin rikon jam’iyyar gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

XS
SM
MD
LG