Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangama Tsakanin Sojoji Da Wasu Fulani a Taraba


Sojojin Najeriya

Hadakar kungiyar makiyayan Najeriya ta maida martani game da kisan da sojoji suka yiwa wasu Fulani makiyaya sama da goma a yankin Katibu, dake karamar hukumar Lau a jihar Taraba.

Tun farko dai rahotanni sun bayyana cewa an kashe fulanin ne a yankin karamar hukumar Lau, wanda daga bisani aka kawo gawarwakinsu zuwa shedikwatar rundunar yan sandan jihar a Jalingo, fadar jihar Taraba.

To amma kuma jim kadan sai ga sanarwar da rundunar sojin kasar ta fitar dake dauke da sa hannun daraktan yada labarai Birgediya Janar Texas Chukwu, wadda ke cewa sojojin sun kashe wasu bata gari goma tare da cafke guda a yankin Numan dake jihar Adamawa wanda kuma dukkaninsu Fulani ne.

A cewar rundunar sojin an kashe mutanen ne bayan musayar wuta da sojoji, haka kuma an samu bindigogi a wajensu.

To sai dai kuma tuni hadakar kungiyoyin makiyaya a Najeriya ta maida martani da cewa akwai abin dubawa a lamarin, inda ta kafa kwamitin bincike.

Mafindi Umar Danburam dake zama mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah a Najeriya, mai kula da jihohin arewa maso gabas, ya ce zasu binciki lamarin.

Wannan lamari dai na zuwa ne a kasa da mako guda da hatsaniyar da ta faru a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma yan kabilar Bachama, a wasu yankunan karamar hukumar Numan dake jihar Adamawa inda aka samu asarar rayuka.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG