Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ARGENTINA: An Zargi Tsohon Shugaban Kasar da Yiwa Wani Bincike Katsalandan


Tsohon shugaban kasar Argentina Carlos Menem

A shekarar 1994 aka kaiwa zauren taron Yahudawa hari wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Yau Alhamis tsohon shugaban kasar Argentina tare da wasu 12 zasu gurfana a gaban wata kotun kasar.

Ana zargin tsohon shugaban da mutanen da yin zagon kasa wa binciken gano wadanda suke da hannun akan harin 1994 da aka kai kan zauren Yahudawa.

Masu gabatar da kara suna tuhumar tsohon shugaban Mr. Carlos Menem da wau 12 da suka hada da babban jami'in leken asiri da wani alkalin kotun tarayya saboda kokarin da suka yi na karkata binciken don kada ya shafi wani haifaffan kasar Syria Alberto Kanoore Edul. Ana kyautata zaton shi Edul din na cikin wadanda suka kai harin.

Mr. Menem dan shekaru 85 ya zamo shugaban kasar Argentina ne a shekarar 1989 kuma yayi shekaru goma yana mulki. Shi ma dan asalin Syria ne. Yanzu shi sanata ne a majalisar dokokin kasar. Mr. Menem dai ya musanta zargin.

Kawo yanzu ba'a taba kama kowa ba akan harin ranar 18 ga watan Yulin shekarar 1994 kan zauren taron Yahudawa a birnin Buenos Aires babban birnin kasar. Harin yayi sanadiyar mutuwar mutane 85 yayin da wata mota shake da bamabamai ta aukawa ginin wanda nan take ya rikito.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG